Philemon

1Bulus, daurarren Yesu Almasihu, da kuma dan’uwa Timotawus zuwa ga Filimon, kaunataccen abokinmu da kuma abokin aikin mu, 2da Afiya yar’uwanmu da Arkifus abokin aikin mu a filin daga, da kuma Ikilisiyar da take taruwa a gidan ka: 3Alheri da salama su kasance gare ka daga wurin Allah Ubanmu, da Ubangiji Yesu Almasihu.

4Kowane lokaci ina gode wa Allah. Ina ambaton ku cikin addu’oi na. 5Na ji labarin kauna da bangaskiya da ka ke da ita a cikin Ubangiji Yesu da dukkan yan’uwa masu bi. 6Ina addu’a zumuntar bangaskiyarka ta inganta ga kawo sanin kowane kyakkyawan abu dake cikin mu a cikin Almasihu. 7Na yi farinciki kwarai, na kuma ta’azantu saboda kaunarka, saboda zukatan masu bi sun kwanta ta wurin ka, dan’uwa.

8Saboda haka, ko da ya ke ina da gabagadi a cikin Almasihu domin in ba ka umarni ka yi abinda ya kamata ka yi, 9duk da haka sabo da kauna, na fi so in roke ka- Ni, Bulus, dattijo, a yanzu kuma ga ni dan kurkuku domin Almasihu Yesu.

10Ina rokon ka saboda da na Onisimus, wanda na zama uba a gare shi sa’adda nake cikin sarkokina. 11Domin a da kam, ba shi da amfani a wurin ka, amma yanzu yana da amfani a gare ka da kuma a gare ni. 12Na kuma aike shi wurinka, shi wanda ya ke a cikin zuciyata kwarai. 13Na so da na rike shi a wuri na, domin ya rika yi mini hidima a madadin ka, a lokacin da ni ke cikin sarkoki saboda bishara.

14Amma ba na so in yi wani abu ba tare da sanin ka ba. Ba ni so nagarin aikinka ya zama na dole amma daga kyakkyawar nufi. 15Watakila dalilin da yasa ya rabu da kai na dan lokaci ke nan, domin ka karbe shi kuma har abada. 16Daga yanzu ba za ya zama bawa ba kuma, amma fiye da bawa, wato kaunataccen dan’uwa. Shi kaunatacce ne musamman a gare ni, har fiye da haka ma a gare ka, a cikin jiki da kuma cikin Ubangiji.

17Idan ka maishe ni abokin hidima, ka karbe shi kamar yadda za ka karbe ni. 18Idan kuwa ya yi maka abinda ba daidai ba ko kuwa kana bin sa wani abu, ka dauka yana wurina. 19Ni, Bulus, na rubuta wannan da hannuna: zan biya ka. Ba kuwa cewa sai na gaya maka cewa ina bin ka bashin kanka ba. 20I, dan’uwa, ka yi mani alheri cikin Ubangiji; ka ba zuciyata hutu a cikin Almasihu.

21Saboda Ina da tabbaci game da biyayyarka, na rubuta maka. Na san za ka yi fiye da abinda na roka. 22Harwayau, ka shirya mani masauki. Domin ina fata ta wurin adu’oinku, nan ba da dadewa ba za a maida ni wurin ku.

23Efafaras, abokina cikin Almasihu Yesu a kurkuku yana gaishe ka, 24haka ma Markus da Aristarkus, da Dimas, da Luka abokan aikina. 25Bari Alherin Ubangiji Yesu Almasihu ya kasance da Ruhunka. Amin.

Copyright information for HauULB